Hisbah Ta Kamo Maza Da Mata Da Ake Zargi Da Yin Wanka Tare A Gidan Chasu A Kano.

Spread the love

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta samu nasarar kamo wasu matasa su 20, da ake zargin suna Chashewa da kuma wanka Maza da Mata a wuri guda.

Dakarun Operation Kauda Badala ne, suka Kai sumamen a MRA SPORT & MORE, dake Ring Road , bayan samun korafe-korafen jama’a kan yadda Maza da Mata suke yin abubuwan da suka Saba da shari’ar addinin musulinci.

Mukaddashin Babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Kano, Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya ce dokar jahar ce ta Hana haduwar Maza da Mata, a cikin ruwa suna wanka a waje daya.

Dr. Mujahiddin Aminuddin , ya bayyana takaicinsa bisa samun Matasan da aka yi, a lokacin da yakamata ace suna yin zikirin juma’a da Neman gafarar Allah, tare da karanta alkur’ani mai girma.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa , Matasan da ake zargi sun shirya bikin Faty ,inda za a yi wanka Maza da Mata tsirara a cikin ruwa.

Hukumar Hisbar ta ce yin hakan ba daidai ba ne, kuma bai dace addinin musulinci ba.

Dakarun Operation Kauda Badalar , sun Kama Maza 17 da kuma Mata 3 , a Gidan Chasun na MRA SPORT & MORE dake Ring road Kano a Ranar Jama’a.

Mukaddashin Babban kwamandan hukumar Hisbar , ya yi Kira ga iyaye , su Kara sanya ido kan yayan su domin sanin wadanda suke mu’amulla da su, don kar abokan banza su Talata tarbiyarsu.

Wasu daga cikin matasan da aka cafko , sun yi nadamar zuwa wajen , inda wasu suka bayyana cewa tsautsayi ya kai su domin cin abinciki.

A karshe hukumar ta ce da zarar ta kammala bincike za ta dauki mataki na gaba kan matasan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *