Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta sake Samun nasarar kama wata mota makare da kwalaben Barasa a cikin ta , kan hanyar Karamar hukumar Madobi dake jahar.
Dr. Mujahidin Abubakar, Wanda shi ne mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, ne ya bayyana hakan a zantawar da suka Yi da idongari.ng, a birnin Kano.
Ya ce yanzu haka motar an Kai ta hukumar don fadada bincike kafin a Gurfanar a gaban Kotu.
A ranar Litinin da daddare sai da hukumar ta kama motar giya akan titin B.U.k. maidauke da kwalaben Barasar 24,000.
Hukumar ta gargadin mutanen da suke kawo giyar suji tsoron Allah , domin Kano gari ne na Ibadah kuma gari ne na masoya Annabi.
Saurari muryar Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar…..