Rundunar yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano, ta lashi takobin ci gaba da yaki da masu kwacen waya da harkar daba da sauran miyagun laifuka a fadin jihar.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan kwanaki kadan bayan daworsa daga wani taro na musamman da ya halatta, a birnin Washington DC dake kasar Amurika.
SP Kiyawa, ya kara da cewa, sun kwashe tsawon makonni biyu suka shafe ana horas da su, don kara musu ilimi kan abunda ya shafi tsaro.
Taron dai an tattara matsakaitan ma’aikata da ake ganin sune manyan gobe a harkar tsaro, na kasashe dabam-daban na Afrika, da suka hada sojoji, yan sanda, jami’an farin kaya da sauran kwararru a fannonin tsaro.
- Dangote ya rage farashin litar man fetur zuwa naira 840
- Kotu Za Ta Duba Yiwuwar Ba Da Belin Tukur Mamu
‘’tabbas da muka je wadanda suka kware sune suka yi wannan horaswa sannan aka tattauna matsalolin tsaro na afrika’’ SP Abdullahi Haruna Kiyawa’’.
Kakakin yan sandan Kanon, ya ce tsawon lokacin sun sami Karin ilimi kuma za su bayar da shawarwari domin inganta tsaro.
Haka zalika ya kara da cewa kamar matsalar fadan daba da kwacen waya da ake fuskanta a jihar Kano, kuma sun tattauna da jama’a da kuma irin hanyoyin da suka bi don magance matsalolin tsaro da suka fuskanta.
A karshe ya ce a wajen bitar an yaba wa Nijeriya bisa jajircewar da take yi wajen yaki da aikata laifuka.