Ƴansanda a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya, sun harbe akalla mutum biyar yayin wata gagarumar zanga-zanga da aka shirya don adawa da shirin kara haraji,a cewar ƙungiyar likitocin ƙasar.
Wani ɗan jarida daga kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ya ga gawawwaki akalla biyar na masu zanga-zanga a wajen majalisar dokokin ƙasar.
Tun da farko, dandazon mutane sun kutsa cikin majalisar ƙasar tare da kaucewa shingayen ƴansanda, inda suka cinna wuta a wani ɓangare na ginin.
Wuta ta kuma ɓarke a wani ɗakin taro a Nairobi.
Aƙalla mutum 40 ne ke kwance a asibiti inda suke samun kulawar likitoci.