Shugaban hukumar alhazan jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya nuna damuwarsa kan ƙarancin sayen kujerun aikin Hajji mai zuwa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yau Talata yayin wani taron haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatan hukumar da da kuma manyan jami’anta na ƙananan hukumomi, a ofishin hukumar da ke Kano, kamar yadda wata sanarwa da kakakin hukumar Sulaiman A. Dederi ya fitar ta bayyana.
Alhaji Lamin ya buƙaci shugabannin hukumar na ƙananan hukumomi da su tashi haiƙan su ƙara azama wajen ganin an sayar da yawan kujerun da aka ware wa yankunansu.
Haka kuma ya yi kira da a samar da dabaru na bunƙasa cinikin kujerun da cimma aikin da ke gaban jihar a kan lokaci.
Hukumar alhazan ta sanya ranar 1 ga watan Janairu na shekara mai kamawa, 2025, a matsayin ranar rufe karɓar kuɗin ajiya na aikin Hajjin na bana daga maniyyata a jihar.