Hukumar Civil Defense Ta Cafke Wadanda Ake Zargi Barnatar Da Wayar Taransifoma A Jigawa.

Spread the love

 

Hukumar tsaron civil defense reshen jahar Jigawa, ta samu nasarar cafke wasu mutane Uku , wadanda ake Zargi da barnatar wayar cable na Taransifoma.

Kakakin hukumar tsaron civil defense reshen jahar Jigawa ASC Badruddin Tijjani ne ya bayyana hakan ta cikin Wani sautin murya da ya aike da Jaridar www.idongari.ng, a ranar Litinin.

Mutanen da Ake Zargin sun hada da Isah Sani Mai shekaru 28, Lawan Umar Dan Shekaru 27 da kuma Mudassir Idi Mai shekaru 21, dukkansu mazauna Garin Keyakko karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne, da misalin karfe 3:30pm na yamma, hukumar ta samu rahoto daga Wani bawan Allah, Mai suna Sabi’u Muhd, inda ya shaida wa jami’an su cewar ya taho daga Babaldo ne don shigar da korafi kan wasu mutane da ya gansu suna yankar wayar Taransifoma.

Badruddin Tijjani, ya kara da cewa , bayan karbar korafin ne jami’an su , suka tafi Garin Babaldo, Inda suka cafko wadanda ake Zargin.

Sai dai Daya Daga cikin wadanda ake Zargin, Mudassir Idi, ya shaida wa jami’an Civil defense, cewar ya siyi wayar akan kudi naira Dubu arba’in, a wajen Isah Sani.

Ya kuma kara da cewa Yana gudanar da sana’ar Siyan kayan Gwangwan.

Kayan Taransifomar da aka barnata, sun Kai naira Dubu dari Uku da tamanin da biyar, Inda babban kwamandan hukumar, Mahammad Danjumma,ya bayar da umarnin gudanar da bincike kafin a Gurfanar da su, a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

A karshe hukumar ta gargadi jama’a kan kaucewa irin wannan aika-aika domin duk Wanda aka sake kama wa za a dauki hukunci Mai tsanani akansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *