Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Kano sun kama wani ma’aikacin banki tare da wasu ‘yankasuwa guda uku da laifin almundahana ta kuɗi a jihar.
An kama mutanen ne a hanyar Unity Road, kasuwar Kantin Kwari a Kano, biyo bayan sahihan bayanan sirri dangane da mutanen da ake zargi da safarar wasu makudan kudade.
Hukumar ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntarta ta X.
Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun ƙware wajen karɓar kuɗaden Naira da suka lalace daga bankuna daban-daban, tare da cire wasu ‘yan kudade daga kowane bandur sannan su ajiye sauran a asusunsu a wani banki na daban inda kuma ma’aikacin bankin da suke aiki tare zai rubuta ajiyar kuɗin a matsayin ainihin cikakken adadin kuɗin da suka amsa
A lokacin da aka kama su, jami’an sun kwato naira miliyan 7.5 daga hannun waɗanda ake zargin.
Hukumar ta ce za a gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.