Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Musanta Zargin Rashin Bai Wa Daurarru Ishesshen Abinci.

Spread the love

Hukumar Kula da Gidajen Yarin Najeriya reshen jihar Kano ta musanta rahotonnin da wasu kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito na rashin bai wa fursunonin da ke ɗaure a gidajen yarin jihar wadataccen abinci.

A baya-baya nan dai an yi ta samun labaran ƙorafe-ƙorafe kan rashin bai wa fursunonin wadataccen abinci a jihar a shafukan sada zumunta.

To sai dai cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gidajen yarin jihar, Musbahu Lawan K/Nasarawa ya fitar ya ce an yaɗa rahotonni ne kawai domin ɓata wa hukumarsu suna.

DANDALIN KANO FESTIVAL

”Waɗannan rahotonni abin takaici ne, kuma hukumarmu na shaida wa al’umma cewa walwala da jin daɗin fusunoninmu shi ne babban abin da hukumarmu ta sanya a gaba, don haka ne koyaushe hukumarmu ke tabbatar wannan muradi duk kuwa da halin matsin tattalin arziki da ƙarsamu ke ciki”, in ji sanarwar.

Ya kuma ƙara da cewa ba abinci kawai  hukumar ke bai wa fursunonin ba, har ma da ilimantar da su da kuma ba su horon sana’o’in dogaro da kai da za su taimaki rayuwarsu bayan kammala zaman gidan yarin.

A Najeriya ana yawan samun ƙorafe-ƙorafe kan halin da ɗaurarru ke ciki a gidajen yarin ƙasar, kama daga kula da lafiyarsu da abinci da kuma babbar matsalar cunkoson fursunoni a gidajen yarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *