Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta ayyana Neman dakataccen kwamishinan aiyuka na musamman na jahar Jigawa, Auwal Danladi Sankara, ruwa a jallo sakamakon kin bayyanar sa a hukumar.
Babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Kano, Asheik Dr Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana hakan a Wani taron manema labarai da ya gudanar da yammacin Litinin.
Ya ce tunda Wanda Ake Zargin yaki bayyana kamar yadda aka Yi alkawari za a sulhunta, don haka ya karya belinsa da hukumar ta bayar tunda farko.
Hukumar ta na Zarginsa da yin mu’amula da matar aure, Inda sakamakon haka ne Gwamnatin jahar Jigawa ta Dakatar da shi, har sai an kammala bincike.
Sai dai mijin matar Mai suna Nasir Buba, ya Garzaya gaban babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Kofar kudu karkashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, Inda ya roki Kotun ta Sanya jami’an Yan Sanda su fadada bincike kan Wanda ake Zargin.
Lauyan Mai kara Barista Haruna Magashi, ya ce suna Zargin Wanda Ake kara da yin mu’amula da matar Nasir Buba, don haka suke son a fadada bincike domin gano wacce irin mu’amula ce.
Anasa bangaren lauyan Wanda Ake Zargin, Barista Saddam Sulaiman Shehu, ya musanta Zargin, harma ya tabbatar da cewa a doka hukumar Hisbah ba ta da madogarar da za ta Gurfanar da Wani a gaban kotun.