Hukumar Hisbah a Kano ta cafke matashin da yan sanda ke ma bisa zarginsa da kwacen wayoyin jama’a.

Spread the love
Zaria Road Na’ibawa Kano

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta samu nasarar cafke wani matashi mai suna, Aminu Lawan mai shekaru 35, mazaunin karamar hukumar Tudun-wada ta jahar, bisa zargin sa da aikata laifin kwacen wayoyin al’umma.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Kano, DR. Mujahid Aminudin Abubakar ne yabayyana hakan ga manema labarai a birnin Kano.

Mujahid Aminudin ya ce, wanda ake zargin jami’an yan sanda sun shafe watanni takwas suna neman sa, sakamakon addabar al’umma da kwacen wayoyin su.

Ya kara da cewa, matashin an kama shi ne a kwanar Dawaki , daya daga cikin yankunan da ya addaba da laifin kwacen kwacen waya.

Aminu Lawan da ake zargin ya bayyana cewa, kwana daya kenan da daworsa daga Port Harcourt, kuma an kama shi ne lokacin da yake yunkurin aikata lalata da wata budurwa a wani Login da ke Kwanar Dawaki.

Ya kuma tabbatar da cewa ya na tare da wadanda suke aikata laifukan kwacen wayoyin jama’ar, amma shi bay a kwata.

Gamayyar hukumomin tsaro a Kano sun tattauna da shugabancin jam’iyun siyasa gabanin zaben cike gibi da za a sake yi a Kunchi/Tsanyawa.

Ƙudirin ƙirƙiro ƴan sandan jihohi ya tsalake karatu na biyu a zauren majalisa

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbah ya ce yanzu haka sun mika matashin ga sashin binciken manyan laifuka na rundunar yan sandan jahar Kano, don fadada bincike akansa.

A karshe Mujahid Aminudin Abubakar, ya jinjina wa jami’an yan sandan jahar Kano, bisa hadin kain da samu daga gare su, wajen gudanar da aiyukan su na yau da kullum.

Tun bayan zuwan kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, a watan Mayun 2023, matsalar kwacen waya ta ragu sakamakon matakan da ya dauka na kulla alakar aiki da al’umma don taimaka mu su wajen dakile matsalar.

Yanzu haka dai jama’a a birnin Kano, su na fito wad a wayoyin salula su rike hannu ba tare da jin tsoro ba ko fargabar wani abu zai faru da su.

IDONGARI.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *