Hukumar Hisbah a Kano ta cafke Ramlat Princess bayan ta tallata kanta a fanfen bidiyo cewar duk namijin da zai aure ta sai ya kawo macen da za su yi latata.

Spread the love

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta kama matashiyar budurwar nan mai suna Ramlat Princess, bayan ta tallata kanta a wani faifen bidiyo tare da yada shi a shafukan sada zumunta.

Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa, An jiyo Ramlat a cikin bidiyon ta na cin alwashin duk namijin da zai aure ta, sai ya auro mata wata macen da za ta dinga yin lalata da ita.

A baya-bayan nan hukumar Hisbar ta sha kai sumame mai taken Kawar da badala, a wuraren da ake zargi ana aikata aiyukan da suka saba da tarbiya da kuma koyar addinin musulinci.

Jahar Kano jaha ce , ta musulinci wadda ta ke tafiya da dokokin shari’ar musulinci, sai dai sakamakon matsalolin rayuwa da kuma zaman banza da rashin aikin yi,  ya sanya wasu matasa sun mayar da shafukan sada zumunta wajen huce haushin su, da yin duk abunda suka da dama.

Idan ba a manta ba, idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewar a ranar talatar da ta gabata, hukumar Hisbar ta kama shahararriyar  yar Tiktok din Murja Ibrahim Kunya, har ta gurfanar da ita a gaban wata kotun shari’ar addinin musulinci tare da aikewa da ita gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya bisa zargin aikata badala, tara batagari cikin dare da kuma tada hatsaniya da daidai sauransu.

Karan ta wannan wannan labarin An gurfanar da Kwastoma bayan ya sace Kudin da ya biya Karuwa.

Karan ta wannan labarin Tinubu na duba yiwuwar kafa ‘yan sandan jihohi

Kawo yanzu dai hukumar ta hisbar ba ta bayyana matakin da za ta dauka ba akan Ramlat Princess, bisa zargin da ake yi mata.

A makon da muke ciki ne Mukaddashiyar babban kwamandan hukumar bangaren mata DR. Khadija Sagir Sulaiman, ta bayyana cewa za su ci gaba kama masu hawa shafin Tiktok suna furta kalaman batsa domin ba za su daga mu su kafa ba.

Al’ummar jahar sun yi fsrin ciki da kamen da hukumar ta fara domin tauna aya don tsakuwa taji tsoro, sakamakon yadda wasu ke zargin akwai shafaffu da mai da ba a iya taba su, wanda hukumar ta musanta zargin tare da cewar babu wanda yafi karfin doka matukar an same shi da aikata laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *