Hukumar Hisbah a Kano Ta Kamo Mata da Maza a gidajen Rawar Solo.

Spread the love

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta sake cafke wasu Matasa 13, a wuraren da ake zargi ana aikata Badala a sassan jahar.

Mukaddashin Babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Kano, Dr. Mujahid Aminuddin Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan kammala sumamen da hukumar ta Kai a daren jiya Alhamis.

Wuraren da hukumar ta kai sumamen, sun hada da gidan Rawar Gala na Na’ima Entertainment a Titin Zengeru, Titin Bama Sabon Gari, Lodge Road, Alu Evenue Road, Titin filin sukuwa, Ja’en, Titin gidan Zoo da kuma yankaba.

Ta Inda Baki Ya Karkata Ne Ya Sanya Sheik Aminu Daurawa Ajiye Mukaminsa

An Maka Alƙali A Kotu Kan Rushe Gidan Marayu A Zariya

An dai samu nasarar cafke Maza 03 da Mata 10 , kuma tambayoyin da jami’an hukumar Hisbah suka yi wa matan , sun bayyana cewar Su ba yan Kano ba ne, kuma sun fito ba tare da sanin iyayensu ba.

Dr. Mujahid Aminuddin ya ce a daya daga cikin gidan rawar Solon, yan matan da suka Kama sun fito daga jahohin Katsina, Gombe, Maiduguri da kuma Yobe, har suka yi alkawarin ba za Su sake aikata wa ba, bayan hukumar Hisbah ta Yi mu Su nasiha.

A karshe ya ce gwiwar Su ba za ta Yi sanyi ba,wajen Ci gaba da yaki da Badala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *