A ci gaba da kai sumame da hukumar Hisbah ta jahar Kano, ke yi, a wuraren da ake zargin Maza da Mata na taru wa don aikata masha’a, a sassan jahar, ta samu nasarar kama matasa 18, a simamen ta mai ta ken, Operation Kauda Badala, don tsaftace jahar daga dukkan munanan aiyuka.
Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Mujahid Aminuddeen Abubakar ,shi ne ya tabbatar hakan ga Idongari.ng, a daren jiya Lahadi.
Dr. Mujahid ya ce, sun kamo maza 9 da kuma mata 9, a yakunan Zangon Dakata, Bakin River Bird Sabon Gari, Airport Road, Titin Asibitin Nasarawa, Alu Avenue, Titin Mumdubawa, Ahmadu Bello Way da kuma Hadejia Road.
Yan bindiga sun kai hare-hare tare da sace fiye da 30 a Kaduna
Ya kara da cewa, cikin wadanda aka kama harda wasu da suka zo daga kasashen waje, domin yin bikin Birthday.
” Yanzu me za a yi da bikin Birthday ana fama da abinda za a ci , amma sai an hada maza da mata an yi bidi’a domin koyi ne da yahudawa”.
Haka zalika rundunar yan sandan jahar Kano, ta turo wa hukumar hisbar wasu matasa 38, da aka kamo su a kasuwar Tumatir ta Kwanar Gafan , wadanda mafi ya wansu suna dauke da juna biyu da kuma masu goyo da suka haifa a Kasuwar .