Hukumar Hisbah a Kano za ta mayar da hankalin ta kan horas da Dakarun ta illimin aikin Hisbah a zahiran ce

Spread the love

Hukumar Hisbah za ta mayar da hankalinta kan horas da Dakarunta illimin aikin Hisbah a zahirance kuma da ki, da ki, tun daga matakan kananan hukumomin 44, har zuwa shalkwata dan kara fahimta da gogewar aiki.

Babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya sanar da hakan a lokacin bikin kaddamar da sabbin mataimakan kwamandojin Hisbah, mata na kananan hukumomin 44 wadan da hukumar Hisbah ta tantance, a kwanan bayani kuma babban kwamandan ya kaddamar da su da a shalkwatan hukumar a unguwar Sharada dan fara aiki gadan gadan.

Mai magana da yawun hukumar hisbah na jahar Kano, Lawan Ibrahim Fagge, ya ce tuni hukumar Hisbah ta fara hada hannu da manyan makarantun kwalejin illimi guda 4 a jihar kano domin fara tsara manhajar koyar da karatun aikin Hisbah, tare da bayar da takardan, satifiket, da na difuloma, da NCE idan dan Hisbah ya kamala za a ba shi.

Ƴan Sanda A Gombe Sun Kama Mutane 23 Bisa Zargin Aikata Laifuka Daban-daban

Wata babbar kotun jahar Kano ta fara sauraren shaidu kan kisan matar da aka zarga da maita

Ya kara da cewar hukumar Hisbah ta sami manyan litattafa guda 3 wadan da duk sunyi cikakken bayani a kan aikin Hisbah, kimanin shekaru 250 da rubutawa, duk sun yi magana a kan aikin Hisbah, wadan da daga litattafan ne za’a rinka koyar da darusan aikin Hisbah.

Daga karshe Sheikh Aminu Daurawa ya shawarci, Dakarunsa, Musaman mataimakan kwamandojin, mata na kananan hukumomin 44 da su zaman masu hakuri da juriya da tsafta kamar takwarorinsu maza.

Da yake karin haske mataimakin babban kwamandan Hisbah Mai kulla da sashin aiyukan yau da kullum, Dr. Mujahid Aminudeen Abubakar ya yi addu’a ga sabbin mataimakan kwamandojin mata tare da Jan hankali kan kula da dokokin aikin Hisbah.

Tun da fari, mataimakiyar babban kwamandan hukumar Hisbah Mai kulla da sashin mata, Dr. Khadija Sagir Sulaiman, ta yi bayani yadda manyan malamai suka yi aikin tantance sabbin mataimakan kwamandojin mata, kamar yadda dokokin hukumar ya tanadar.

Dr. Khadija Sagir Sulaiman ta ce daga yanzu sabbin mataimakan kwamandojin mata na kananan hukumomin 44 za su kasance karkashin, Babban kwamandan hukumar Hisbah na jiha bugu da Kari daga gareshi za su rinka karban ummarnin gabatar da aikin Hisbah.

A jawabinta a madadin sabbin mataimakan kwamandojin Hisbah mata na kananan hukumomin 44, mataimakiyar kwamandan karamar hukumar Dala, malama khadija Balanti Cediyar yan gurasa ta yi alkawarin za yi aiki tukuru kamar sauran takwarorinsu maza, tare da addu’a ga hukumar Hisbah.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *