Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta samu nasarar damke jarumar TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya.
Wata majiya daga Hukumar Hisbah ta shaida wa jaridar Idongari.ng, cewar an kama Murja Kunya ne biyo bayan ci gaba da yin abubuwan rashin da’a , da suka saba da koyar war addinin Musulinci.
Majiyar ta kara da cewa, a baya an yi mata nasiha tare da lura da irin abubuwan da ta ke aikata a shafukan sada zumunta sai dai ba ta sauya wa, hakan ne ya sanya hukumar kama ta.
Jarumar Tiktok din dai ta shahara, wajen furta kalaman batsa da na rashin tarbiya da kuma sanya sutura da ta saba wa addinin musulinci da al’adar Hausawa tare da kwaikwayon wasu al’adu na daban.
Karan ta wannan labarin Hisbah ta kwace kwalaban giya, ta kama mata masu zaman kansu a Kano
Tun a baya dai jama’a da dama ke ganin baikon hukumar Hisbar na kin kama Murja Kunya sakamakon yadda ta shafa wa idon ta da toka, ta ke shuka rashin mutunci a shafukan sada zumunta, iya son ranta.
za mu kawo mu ku karin bayani…….