Hukumar Hisbah Ta Jahar Kano Ta Gana Da Mamallaka Gidajen Event Center

Spread the love

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta yi wani zama, na musamman da kungiyar ma su ( Event Center) don tsaftace harkokin Bukukuwan Aure, yadda ya dace da shari’ar musulinci.

Babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Sheik Mallam Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya jagoranci taron tattaunawar , a shelkwatar hukumar dake Sharada.

Sheik Daurawa, ya ce sun karbi korafe-korafe ma su Yawa , wadanda suka shafi matsalolin Aure, kuma shi ne yake ci wa hukumar Hisbah tuwo a kwarya.

Mukaddashin kwamandan hukumar Hisbah Dr. Mujahiddin Aminuddin Abubakar, ya kara da cewa, tattaunawar ta zama dole sakamakon yadda ake samun tabarbarewar tarbiya da kan haifar da matsaloli a cikin zamantakewar auren.

Ya ce yin bukukuwa Halal ne, amma ba a yarda a hada maza da Mata ba, ko yin shigar da bata dace ba, da kuma wadanda suke barin gidajen iyayensu ko mazajensu, har sukai tsakar dare ba tare da sun dawo ba.

Dr. Mujahiddin Aminuddin, Ya Kara cewa sun gano cewa ba a bin ka’idar Hisbah , shi yasa suka ga ba za su iya kyalewa a ci gaba da aikata Badala ba kamar yadda jaridar idongari.ng, ta ruwaito.

Sai dai hukumar Hisbah, ta ce zaman da suka yi sun gano cewar masu kakanan Event Center ne sukafi karya dokar, kuma nan gaba kadan za su wayar da kan al’umma kan illar yin dare a wajen bukukuwa ko shiga da makami da kayan maye da kuma kiyaye lokutan sallah da dai sauransu.

Shugabar kungiyar ma su gidajen Event Center, Hajiya Fatima Abdussalam, ta bayyana cewa suna murna da wannan gayyata da hukumar Hisbar ta yi, kuma suna jajircewa wajen bin dokokin.

Sai dai sun bukaci hukumar ta Goya mu su baya, wajen fadakar da iyaye da sauran al’umma harma da Masu gidajen event center bin doka da oda.

IDONGARI.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *