Hukumar hisbah ta jahar Kano, tare da hadin gwiwar jami’an hukumar Karota , sun kama wata mota dauke da giya akan titin B.U.K Road dake jahar.
Mukaddashin babban kwamandan hukumar hisbah na jahar Kano, Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar , ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifen murya da ya aike wa da IDONGARI.NG, a ranar Talata 20 ga watan Augusta 2024.
Dr. Mujahidin Aminuddin, ya ce an kama motar ce a ranar Litinin da daddare, da misalin karfe 1:00am na dare.
” Jiya da daddare wajen karfe daya na dare, jajirtattun jami”an mu sun Yi nasarar kama motar giya bayan Samun bayanan sirri.
Motar da Ake Zargin ta dauko Kiret 1000 na giya, wadda tuni an Kai motar ofishin hukumar hisbah don fadada bincike akan ta kafin a Gurfanar a gaban Kotu.