Hukumar Hisbah ta kama Wasu Yara da ke Roƙo da Barace-Barace a Kano

Spread the love
Kano Hisbah

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano Reshen ƙaramar hukumar Dala, ta kama wasu ƙananan yara masu Roƙon Kuɗi da barace-barace akan titunan birnin Kano.

Ofishin Hisbah na Ƙaramar Hukumar Dala ƙarƙashin Jagorancin Kwamanda Malam Umar Bala Muhammad sune suka yi wannan kamen yayin wani samame da suka gudanar a wasu tituna na karamar hukumar.

Da yake bayani a zantawarsa da manema labarai a ofishin hukumar, Kwamandan Malam Umar Bala ya ce; Kamen na zuwa ne Bayan wasu Ƙorafe-ƙorafe da al’umma suke kaiwa ofishin hukumar ga me da yawaitar yaran akan tituna wanda ko makaranta wasu basa zuwa saidai leƙa motoci suna Roƙon Kuɗi da yawon barar a titi.

Ya kara da cewa, hukumar ta daɗe tana nusar da yaran dama malamansu ko kuma iyayen su kan Haɗarin dake tattare da yawon Bara a titunan sakamakon Rashin sanin Dawa yaron zai yi mu’amala.

“Irin wannan ɗabi’a tana da haɗari matuƙa saboda a irin haka ne ake Zargin wasu na amfani da wannan dama suna sace yara suna kaiwa wasu yankunan kuma suna sauya musu addini da ɗabi’u”.

Sakin Murja Kunya daga gidan yari ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta

 

Yan bindiga sun kai hare-hare tare da sace fiye da 30 a Kaduna“Yanzu haka a ofishin mu akawai wani yaro wanda aka tsinta aka kawo mana shi zancen da nake ya haura wata biyu, munyi cigiyar malaminsa da iyayensa amma shiru har a shafukan sada zumunta muka saka cigiyarsa amma har yanzu malaminsa baizo ba haka ko a iyayen sa babu wanda ya neme shi “.

Wani daga cikin Malaman yaran wanda ya nemi a sakaya sunan sa ya ce suna goyon bayan hukumar Hisbah akan wannan aiki na hana roƙo da barace barace a tituna amma akwai wani ƙalubale da suke fuskanta.

“Iyayen yaran suna taka rawa Sosai wajen ƙara yawan masu Roƙon kuɗi da bara saboda yanzu basa iya kula da ƴaƴan nasu, mu kuma ba kamar Malaman karkara ba wanda suke noma har su taimakawa yaran da abinci “.

Ya ce, Suma gidajen da yaran suke barar abinci yanzu kowa ta kansa yake ba kowa ne yake samun abincin ba balle ma ya bawa Almajiri, shine ma yasa yaran suke tsince – tsincen ƙarafuna su sayar.

Kwamandan hukumar ya ƙara da cewa, wannan hanya ce mai sauƙi da masu satar mutane zasu iya amfani da ita wajen kwashe yaran da suke gararamba a titi, saboda babu wanda yake neman su idan ba’a gansu ba.

A nata Ɓangaren Kwamandar Ɓangaren mata a ofishin hukumar na Dala Malama Hadiza Balanti Cheɗiyar ‘yan Gurasa ta ce, “ya kamata iyaye ku dinga tuna cewar ƴaƴa amana ce da Allah ya bamu don haka ya zama wajibi mu kula da wannan Amana, ku kuma Malamai duk mahaifin da ya gaza kula da yaron sa bayan ya kawo shi to ku mayar masa da ɗan sa”.

A ƙarshe Kwamandan ya ce daga yanzu hukumar zata cigaba da aikin sanya ido don kawo ƙarshen wannan matsala ta yawan ɓarace baracen yaran da rokon kudi a titi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *