Hukumar Hisbah da takwararta da ke kula da, Gidan adana Namun Daji, wato gidan Zoo na jihar kano, sun kammala shiri wani tsaf dan inganta alakar aiki a tsakanin su dan kawar da yada dabi’u da ka iya gurbata tarbiya da al’ada, Musaman a lokacin bikin kirsimeti da ta sabuwar shekarar miladiya da ke gabato wa da ma sauran bukukuwa a nan gaba.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Hisbah Lawan Ibrahim Fagge ya raba wa manema labarai , ya ce babban Daraktanta hukumar (DG), Alhaji Abba Sa’id Sufi shi ne ya sanar da hakan ta cikin jawabinsa a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar jami’in da ke kula da gidan Zoo, karkashin jagorancin Shugaban hukumar, Alhaji Sadik Muhammad kura a shalkwatan hukumar da ke unguwar Sharada kano.
Alhaji Abba Sa’id Sufi ya ce inganta alakar aikin zai ba wa hukumar Hisbah damar sanin irin bukukuwa da tarurraka da jama’a ke gudanarwa baya ga sa ido a tsakanin ma su kai ziyara gidan Zoo dan shakatawa.
Ya kuma yi alkawarin sa ke tura karin jami’ai a karamin ofishin Hisbah da cikin gidan Zoo, ma su cike da kwarewar aiki, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.
A na ta jawabin mataimakiyar babban kwamandan bangaren mata (DCG Women) Dr. Khadija Sagir Sulaiman ta ba yya na farin ciki da ziyarar.
Dr. Khadija Sagir Sulaiman ta bukaci Shugaban hukumar da ke kula da Gidan adana Dabbobin Daji , gidan Zoo da ya dauki mata aiki a hukumar duba da mata da yara su ne su kafi kai ziyara a kowane lokaci gidan Zoo.
Tun da fari a jawabinsa Shugaban hukumar kula da Gidan adana Dabbobin Dajin, Alhaji Sadik Muhammad kura ,ya ce makasudinsa na zuwa hukumar Hisbah shi ne inganta alakar aikin a tsakanin hukumomin guda biyu tare da zamantar da yin aiki tare.
A lokacin ziyarar ya roki hukumar Hisbah da ta kara yawan Dakarunta da ke aiki a gidan Zoo, duba da yadda su ke gudar da aiki cikin kwarewa, tare da alkawarin ba da hadin Kai da goyon baya.