Hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta fara rufe shagunan da ake caca a jihar, waɗanda ta ce suna hada-hada ba bisa ƙa’ida ba.
“Kamar yadda kuka sani, caca haramun ce a Musulunci,” in ji Mujahid Aminudeen mataimakin shugaban Hisbah.
Samamen da suka kai ya biyo bayan ƙorafin shugabannin al’umma da kuma iyaye suka yi cewar caca na neman zama jaraba da ƴaƴansu.
A rana ta farko na samamen, an rufe shaguna 30 a unguwa ɗaya kuma an gargaɗi masu shagunan su yi hattara, kamar yadda jami’in Hisbah ya bayyana.
Malam Aminudeen ya yi gargaɗin cewa Hisbah za ta ci gaba da rufe irin waɗannan shagunan kuma za ta hukunta duk wanda ya saɓa doka.
Shagunan caca da na giya na gudanar da harkokinsu a yankunan da Kiristoci ke zaune a Kano amma Hisbah kan ɗauki mataki idan har ta fahimci akwai Musulmi masu ziyartar irin waɗannan wuraren.
Amma dai samamen na wannan karon, a yankunan da Musulmi ke zaune ne kawai.
- Bello Turji Ya Nemi Sulhu Da Gwamnati
- Kotu Ta Yanke Wa Matashin Da Aka Samu Da Laifin Satar Kayan Abinci Hukunci
Akwai shagunan cacar ƙwallon ƙafa a Kano inda galibinsu ke da talabijin da ake nuna ƙwallon ƙafar Turai.
Malam Aminudeen ya ce sun daɗe suna da ido a kan harkokin shagunan cacar waɗanda a waɗansu lokuta suke ɓatar da sawu.
“Ba su da lasisin gudanar da harkar, saboda lasisinsu na buga gyam ɗin bidiyo ne kawai amma sai su ɓuge da mayar da su shagunan caca,” in ji mataimakin shugaban Hisbah.
Shagunan caca na ƙara samun karɓuwa a Najeriya kuma mutane da dama na ziyartarsu.
An kai samamen ne a garin Minjibir inda baƙi ke tururuwar zuwa.
“Ina baiwa masu waɗannan shagunan su rufe ko kuma mu kama su mu gurfanar da su a gaban kotun Shari’a,” in ji Aminudeen.
Har yanzu dai babu tabbas kan irin hukuncin da za a yanke wa masu shagunan da aka rufe.