Hukumar Hisbah Ta Kulle Gidan Da Ake Zargin Ana Aikata Badala Bayan Fitar Wani Faifen Bidiyo.

Spread the love

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta fitar da sakamakon binciken da ta Yi kan faifen Bidiyon da wata Matashiya Mai suna Nana Haruna wadda akafi sani da Nancy, ta yada a shafukan sada zumunta, Inda ta Yi Zargin cewar ana aikata Badala a Wani gida dake unguwar Kofar Kabuga.

Binciken da hukumar ta gudanar ta gano cewar gidan na wasu marayu ne da wasu Dillalai suka bayar da hayarsa.

Rahotanni na cewa hukumar Hisbar ta rufe gidan da kwado, kuma zai ci gaba da zama karkashin kulawar Hisbah da mamallaka gidan da kuma Yan kwamitin unguwar.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Wannan dai na zuwa ne bayan zaman da hukumar Hisbar ta yi, da matashiyar da kuma Wadanda ta ambaci sunayensu a matsayin su, Wanda babban kwamandan hukumar Hisbah Asheik Dr Aminu Ibrahim Daurawa ya jagoranci zaman.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbah Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya ce Nana Haruna da kuma Wadanda lamarin ya shafa sun San juna, domin ta taba zama a gidan Daya Daga cikinsu Inda ta koma Wani gida bayan sun rabu.

Idongari.ng, ta ruwaito Nana Nancy , yanzu haka tana sana’ar dinkin hula, kuma ta taba yin aure harma ta na da yara, kuma Hisbar ta Kudiri aniyar Mayar da ita garinsu wajen iyayen ta.

A makon da muke ciki ne Nancy ta wallafa Bidiyo, har ta Yi bayanin yadda Ake aikata Badala a gidan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *