Hukumar Hisbah Ta Tura Dakarun Ta Don Hana Hawa Kwale-kwale Da Magriba A Kano.

Spread the love

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta Bai wa kwamamdojinta na kananan hukumomi 44 , umarnin tura dakarun da za su dinga Sanya Ido, a dukkan wuraren da ake daukan mutane a tsallakar da su a kwale-kwale.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Kano, Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar ,ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labari a ranar Alhamis.

Dr. Mujahidin, ya ce sun dauki wannan mataki ne sakamakom labarukan da suke zuwan mu su, marasa Dadi wadanda suke taba zuciya , shi yasa hukumar ta Yi duba kan irin wannan lamari da ake ciki na rasa rayukan mutane.

Ya kara da cewa hatta gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf , abun ya dame shi matuka, hakan ya Sanya hukumar Hisbah fara daukar mataki a dukkan Inda Ake da Koramu ko ruwan da ake haurewa da Kwale-kwale, a fadin jahar za a dinga tsayar da daukar mutane da misalin karfe 6:00pm na yammacin kowacce rana.

” Hisba za ta a jiye mutanen ta idan magriba ta kusa ba za a yi Lodi ba , hakama idan mutanen sun Yi yawa ba za a Yi Lodi ba , idan ruwa ya Kai fiye da Inda yake Shima ba za a yi Lodi ba” Mujahidin Abubakar”.

Saurari muryar Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar

Hukumar ta ce irin wadannan Abubuwan sune suke ta janyo rasa rayukan al’umma.

A karshe hukumar ta Yi addu’ar Allah ya ji kan dukkan wadanda suka rasa rayukan su a sanadiyar kifewar kwale-kwale a fadin jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *