Hukumar kare hakkin mai siye da amfani da kayayyaki ta jihar Kano,karkashin jagorancin shugabanta, Dr Umar Garba, ta karbe wasu kayayyakin abinci da wa’adin amfani da su ya kare, a ci gaba da kai sumame da jami’an hukumar ke yi a sassa dabam-daban na jihar.
babban sakaren zartarwa na hukumar, Alhaji Zangina Jafaru, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aikewa da manema labarai.
Hukumar ta ce an kama kayan ne a kasuwar Singa, wadanda jumullar kudinsu ya kai sama da naira miliyan biyar, a gagrimun aikin da jami’ansu suka yi.
- An Samu Raguwar Fadan Daba Da Kwacen Waya Sosai A Kano
- Asibitin Best Choice Zai Fara Manya Manyan Tiyatu Akan Kuɗi Kaso 50% Bayan Fara Bude Fayil Kyauta Da Rage Kuɗin Ganin Likita Da Ayyukansu
cikin kayayyakin da hukumar ta karbe sun hada da, Madara da Lemuka, wadanda wa’adin amfani da su ya kare.
Haka zalika hukumar ta yi kira ga jama’a da su dinga kula da irin kayan da suke siya, domin kar su sayi wanda wa’adin amfani da ya kare , inda hakan zai yi illa ga lafiyarsu.
A Karshe hukumar ta yabawa gwamnatin Kano da kuma mutanen da suke fallasa masu sayar da kayan da wa’adinsa ya kare ga jama’a , da su ci gaba da bankado su don kare lafiyar mutane daga cimakar yau da kullum.