Hukumar Karota ta bayar da wa’adin awanni 44 ga yan kasuwar da suke kasuwanci kan gadar Kurna Babban Layi da Gadar Kurna Yandoma .

Spread the love

Hukumar kula da zirga zirgar Ababen hawa ta jiha Kano, wato Karota ta bayar da wa’adin awanni Arba’in da hudu (44) ga yan kasuwar da suke kasuwanci kan gadar Kurna Babban Layi da Gadar Kurna Yandoma da su daina.

Shugaban Hukumar Karota Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a yau, lokacin da ya tura tawagar jami’an Hukumar KAROTA a karkashin jagorancin Daraktan Ayyuka na Musamman Malam Tasiu Gambo domin ganin halin da gadojin suke ciki, tare da bayar da umarnin tashin su daga wurin.

Hukumar ta umarce su da su gaggauta tashi daga gurin domin kuwa, ba a yi gadar domin a kasa kaya ba.

A jawabansu daban daban shuwagabannin wajen sun bayar da tabbacin yin biyayya ga umarnin gwamnati kafin cikar wa’adin da aka saka musu.

Alummar unguwannin ne suka yi korafi dangane da kasuwancin da ake yi a kan gadojin.

Haka kuma tawagar Hukumar ta karasa kasuwar Rimi, ta umarci masu kasa kaya a kan titi da su daina kafin Hukumar ta dauki matakin kwashe kayan masu kunnen kashe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *