Hukumar Kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano ( KAROTA), ta sami nasarar kama motoci guda hudu kirar J5 makare da giya.
Shugaban hukumar Karota, Hon. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana hakan a daren jiya Talata, lokacin da yake duba motocin da jami’an Hukumar suka cafke.
Kakakin hukumar Karota na jahar Kano, Nabilusi Abubakar
K/Na’isa, ya ce Hukumar ta sami nasarar kama motocin ne bayan rahotonnin sirrin da suka
a wajen wasu masu kishin jihar Kano.
Ya ce dokar jihar Kano ta haramta shan giya a ko wanne lokaci, musamman yanzu da ake cikin wata mai alfarma
Ya kara da cewa Ya zama wajibi Hukumar ta rubanya kokarinta wajen sa ido a daukacin titinan jihar Kano.
A karshe ya yaba wa jami’an da suka sami nasarar cafke motocin, inda ya ce da zarar an kammala binciki za a mika Giyar Hukumar Hisbah domin ta kara fadada bincike tare da daukar mataki na gaba.