Hukumar Karota ta musanta labarin da ake yadawa na hana kasuwanci a kasuwar Rimi Kano

Spread the love

Hukumar Kula da Zirga zirgarni Ababen Hawa ta jihar Kano, wato  Karota ta musanta jita-jitar da wasu  ke yadawa da cewar Hukumar ta hana gudanar da hada-hadar kasuwanci a kasuwar Rimi.

Hukumar ta Karota ta ce bata  hana kowa ya yi kasuwancinsa ba, amma dole ne kowa ya bi tsarin doka da oda.

Kakakin hukumar na Karota Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar ta fito fili ne domin musanta jita-jitar da ake yi na hana kasuwancin a kasuwar ta Rimi bayan da jita-jitar hana kasuwancin ta karade kafafen sada zumunta .

Hukumar ta ce kowa ya ci gaba da gudanar da kasuwancinsa amma ya zama wajibi a daina kasa kaya a kan titi saboda gujewa afkur hadura da cunkoson hanya.

Hukumar ta KAROTA na godiya da hadin kan da Shugabancin kasuwar ke bayarwa a duk lokacin bukatar hakan .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *