Yayin da muka kusanto watan Ramadan mai alfarma, Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa jiha ta (KAROTA) na kira ga duk masu amfani da hanyoyi, musamman direbobi, da su yi tuki cikin natsuwa da hakuri. Watan Ramadan lokaci ne na ibada wanda ke kawo sauyi a dabi’un tuki sakamakon gajiya, rashin ruwa a jiki, ga kuma yawaitar cunkoso a hanyoyi, musamman a lokacin buda baki da sallar Taraweeh.
Domin kare lafiyar kowa a hanyoyi, Hukumar KAROTA na shawartar direbobi da su bi waɗannan ka’idojin a lokacin Ramadan.
Gudun Wuce sa a Kafin shan ruwa domin wasu direbobin suna gaggawar komawa gida don yin buda baki, wanda hakan ke haddasa cinkoso a titina
- An Umarci Masu Gidajen Rawar Gala Da Wasanni Su Rufe A Kano
- An Kama Mutane 17 Da Zargin Shirya Tayar Da Tarzoma A Kano
Kasance mai Hankali da Nutsuwa domin Azumi na iya haifar da gajiya ko jiri. Idan ka ji kasala, ka dakata ka huta kafin ka ci gaba da tafiya.
Yi Hakuri da Ladabi a Hanya: A lokacin Ramadan, cunkoson ababen hawa yana karuwa, musamman a kusa da kasuwanni da masallatai, ku guji tukin ganganci kuma ku yi wa juna uzuri.
Shan Ruwa da Cin Abinci Mai Sauƙi Kafin Tafiya: Tabbatar da cewa ka sha isasshen ruwa da cin abinci mai sauƙi a lokacin Sahur domin ka samu ƙarfi da kuzari yayin tuki.
Kula da Masu Tafiya a Kafa da Masu Amfani da Keke: Yawancin mutane suna tafiya zuwa masallatai, musamman da daddare. Ku yi tuki a cikin nutsuwa, musamman a yankunan da ake da yawan mutane.
Shirya Tafiyarka Tun Da wuri domin Idan zai yiwu ka guji fita a lokacin cunkoso kuma ka yi tuki a lokacin da kake cikin koshin lafiya.
Bi Dokokin Hanya da Umarnin Jami’an KAROTA: Kowa ya kiyaye iyakar gudu, kuma ya bi doka don kare rayuwaka da ta waninka
KAROTA tana ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron hanya a lokacin Ramadan, kuma za ta ƙara yawan sintiri don tabbatar da ingantaccen zirga-zirga. Muna roƙon dukkan direbobi da su yi amfani da watan Ramadan ta hanyar hakuri, girmama juna, da kuma tuki cikin nutsuwa.
Hukumar KAROTA karkashin jagorancin Hon Faisal Mahmud Kabir na yi wa kowa fatan alkhairi da fatan za a shiga cikin watan Ramadan lafiya
Signed
Nabilusi Abubakar
K/Na’isa
Public Relations Officer
KAROTA
27th Feb, 2025.