Hukumar Kasa Da Tsare-tsare Ta Jihar Kano Ta Yi Kira Ga Jama’a Su Sabunta Takaddun Mallakar Filaye Da Gidajensu Don Gudun Yin Asara

Spread the love

Hukumar kasa da tsare-tsare ta jihar Kano , ta bayyana cewa ranar 31 ga watan Janairun 2025, shi ne wa’adin karshe don sabunta takaddun in filaye da gidaje.

Kwamishinan kasa da tsare-tsare Abduljabbar Muhammad Umar Garko, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a.

Kwamishinan ya yaba wa al’ummar jihar bisa hadin Kan da suke bayarwa wajen sabunta takaddun mallakar.

Abduljabbar Muhammad Garko, ya sake yin kira ga mutane dukkan wadanda za su sabunta takaddun mallakar filaye da gidajensu su gaggauta zuwa ma’aikatar KANGIS don yin hakan.

Ya kara da cewa daga ranar 18 ga watan Disamban 2024 jama’a sun amsa Kiran Inda aka samu fiye da mutane Miliyan Daya wadanda suka Yi rigista daga sassan kananan hukumomin Kano 44.

Ya Kuma ce ya kamata jama’a su Sani cewar ma’aikatar KANGIS Kofar ta a bude ta ke , don su zo su sabunta takaddun su ko kuma ta shafin yanar gizo.

A karshe ya ce al’umma su zo su sabunta takaddun Kafin karshen wa’adin ranar 31 ga watan Janairun 2025 ya kare don kar su Yi asarar filayensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *