Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce tana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobara a wani rukunin shaguna abin da yayi sanadin kowarsu.
Al’amarin dai ya auku ne cikin dare a unguwar Zawaciki a karamar hukumar Kumbotso inda al’amarin ya yi sanadin asarar dukiya ta milyoyin nairori.
Bayanai na cewa ana yawan samun tashin gobara a jihar Kano, inda jami’in hulda da jama’ar hukumar kashe gobara a jihar Saminu Abdullahi, ya ce wutar na yawan tashi ne saboda amfani da wutar lantarki da ba bisa ka’ida ba.
Ana binciken gano waɗanda suka ciri miliyoyi a bankin EthiopiaEthiopia
Za a gina babbar cibiyar lantarki mai amfani da rana a Najeriya