Hukumar Kashe Gobara Ta Bayyana Musabbabin Tashin Gobara A Kasuwar Yan Katako Brigade A Kano

Spread the love

Hukumar kashe gobara ta jahar Kano, karkashin jagorancin babban Daraktan ta, Alhaji Hassan Ahmed Muhd, ta karbi kiran gaggawa daga wani jami’in dan sanda mai suna ASP U.I. Bushira , dake aiki a ofishin yan sanda na Dakata, inda ya sanar da su iftila’in tashin Gobara a kasuwar Brigade Yan Katako, da misalin karfe 1:51am na daren jiya Laraba 13 ga watan Nuwamban 2024.

Kakakin hukumar kashe gobara na jahar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce bayan zuwan jami’an hukumar kashe gobarar sun tarar da wasu shaguna guda biyu wadanda suka kama da wuta, har suka samu nasarar shawo kan lamarin.

Sai dai wutar ta sake tashi a wasu shagunan guda biyu, a wajen da wutar ta fara tashi da farko , kuma jami’an sun yi kokarin tsayar da wutar a iya shaguna hudu da suka tabu ba tare da ta ci gaba da yaduwa zuwa sauran shagunan ba.

Saminu Yusuf ya kara da cewa , gobarar ta tashi ne sakamakon dawo da wutar lantarki, kuma akwai wata na’urar wutar lantarki da ba a kashe ba, wanda shi ne musabbabin tashin wutar.

Saurari muryar ACFO Saminu Yusuf Abdullahi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *