Hukumar kashe gobara reshen jahar Kano, ta fitar da alkaluman kiraye-kirayen da ta samu sakamakon ibtala’in tashin gobara da aka samu a cikin watan Nuwamban da ya gabata.
Kakakin hukumar kashe gobara na jahar Kano, PFS Saminu Yusif Abdullahi ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a jahar birnin Kano.
Sanarwar ta ce sun samu kiraye-kiraye guda 57 tare da samun nasarar tseratar da mutane 12 , sai kuma kiraye-kirayen karya da suka samu guda 7.
Saminu Abdullahi ya kara da cewa an yi asarar dukiya ta sama da naira miliyan arba’in da uku da dubu dari bakwai da tamanin da dari bakwai ( 43,780,700 ) a cikin watan nuwamban 2023.
Haka zalika an samu nasarar tseratar da dukiya ta sama da naira miliyan dari da hudu da dubu dari da ashirin da daya da dari uku ( 104,121,300.), yayin da aka rasa rayukan mutane biyu da ceto mutane 15 da ransu.
A karshe saminu Yusuf yaja hankalin al’umma musamman a wannan lokacin na sanyi da su kiyaye wajen yin amfani da wuta.