Hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta jihar Bauchi ta ce ta damƙa wa dangin wasu mutane da hatsari ya ritsa da su a kan hanyar Bauchi zuwa Toro, kuɗi naira 1, 680,700, mallakar ‘yan uwan nasu.
Rilwanu Sulaiman Birnin Kebbi, jami’in wayar da kai na hukumar ya ce kuɗin mallakar mutum uku ne, a cikinsu har da wanda yake da naira 1, 648, 500.
Ya ce hukumarsu ta damƙa kuɗin ne ga dangin waɗanda suka mutu a ofishinta da ke yankin Toro, bayan kammala bincike a ranar Litinin.
Hatsarin dai ya yi muni, wanda Rilwanu Sulaimanu ya ce ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu, yayin da uku suka jikkata kuma suna kwance suna jinya a asibiti.
Hatsarin mota kusan ruwan dare ne a Najeriya, inda ɗumbin mutane suke mutuwa a kan tituna sanadin karon ababen hawa da sauran dalilai.
- Kungiyar Yaki Da Rashin Adalaci ( WAI) Ta Gamsu Da Hukuncin Da Aka Yanke Wa Frank Geng
- Za A Naɗa Ɗan Kwankwaso Kwamishina A Kano