Hukumar Kiyaye Hadura Reshen Jahar Kano Ta Kaddamar Da Gangamin Wayar Da Kan Al’umma Kan Illar Yin Tukin Ganganci.

Spread the love

Hukumar kiyaye hadura ta kasa ( FRSC) reshen jahar Kano, ta kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a, don fadakar su yadda za su Yi amfani da Ababen hawansu, don kaucewa yin Tukin ganganci.

Da yake gabatar da jawabinsa kwamandan hukumar reshen jahar Kano, CC Umar Masa’udu Matazu, Wanda ya samu wakilcin DCC Hussaini Sulaiman, ya Bayyana muhimmancin wayar da kan al’ummar , don kaucewa yin Tukin ganganci Wanda hakan yake haifar da haduran dake janyo rasa rayukan Fasinjoji ma su yawa fiye da Direban motar.

Hukumar dai ta Saba gudanar da irin wannan gangamin a watanni hudun kowacce shekara, sakamakon yawan Samun karuwar Zirga-Zirgar Ababen hawa, wanda hakan yake Sanya wa a samu karuwar hadura da rasa rayuka da kuma dukiya Mai tarin yawa.

A cewar hukumar ta fito da Sabon salon fadakar da jama’a , Wanda abaya suke shiga Tashoshin Motoci , Amma a wannan shekarar sun raba Abubuwan zuwa gida Uku, da suka hada da ganawa da Yan Jaridu don su isar da sakon ga al’umma gaba Daya.

Haka zalika, akwai gangamin yin jerin gwanon motocin hukumar don shiga Kasuwanni da Tashoshin Motoci don fadar da al’umma.

FRSC , ta kara da cewa haduran da Ake samu fasinjoji masu yawa suna rasa rayukan su, inda shi kuma Direba daya ne ke rasa ransa.

” Zaka ga idan an Yi hadari ana Samun Mutuwar fasinjoji 20 ko 30, Amma kuma Direba daya ne.

Dan haka ne hukumar taja hankalin al’umma, don su gane cewar fasinja Yana da hakkin ya Sanya idanu tare da yin magana idan yaga ana yin Tukin ganganci, domin idan an Yi hadarin Bai San Inda zai tsinci
Kansa ba.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa an Yi wa gangamin na wannan shekarar, ta ke da ” Ka Yi wa Direba magana” idan ta ganshi ya na Tukin ganganci ko gudun wuce Sa’a.

A karshe hukumar ta Yi kira ga masu Ababen hawa, da su daina amsa waya a lokacin da suke Tuki ko Shan Wani Abu tare da kaucewa yin Tukin ganganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *