Hukumar kare hakkin mai siye da mai siyarwa ta Jihar Kano ta ce zata yi aiki kafada da kafada da Yan Jarida na Jihar Kano, domin tabbatar da tsaftace harkokin siye da siyar a fadin jihar.
Sabon shugaban Hukumar Dr. Umar Garba Haruna, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da wakilan kafafen yaɗa labarai na Jihar Kano.
Ya ce idan aka yi La’akari da irin yadda wasu kayayyaki marasa inganci suke bazuwa a kasuwanni akwai bukatar kafafen yaɗa labarai su ci gaba da wayar da kan al’umma game da yadda za su kare kansu daga irin gurɓatattun abubuwan dake yawo a kasuwanni.
Dr. Umar Garba Sheka ya kuma yabawa tawagar manema labaran da suka kasance a yayin tattaunawar musamman bisa yadda ya ce suna bayar da cikakkiyar gudunmawa wajen wayar da kan al’umma.