Shugaban hukumar kwashe shara ta jahar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, ya jagorancin aikin feshin maganin sauro, a yankin unguwar Badawa dake karamar hukumar Nasarawa , domin kawar da sauro da sauran kwari wadanda suke sanya wa al’umma cutar Maleriya.
Ahmadu Zago, wanda Darakta Admin, Alhaji Yahaya Sani Abbas, ya wakilta, ya ce sun kaddamar da aikin feshin maganin sauron a yankin Badawa, don dakile cutukan da sauron ke yada wa ga al’umma.
Ya kara da za a tabbatar an yi feshin maganin lungu da sako na unguwar Badawa, kamar yadda gwamanan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya kudiri aniyar hidimta wa al’umma ta bangarori da dama don samun nutsuwa da walwala a gidajen su.
‘’ Insha Allah za a ci gaba da yin wannan aiki lokaci zuwa lokaci’’ Zago’’.
Masu gidajen burodi sun janye yajin aiki a Najeriya
Gwamnatin Kano ta bankado haramtattun gine-gine 68
Sai dai Haruna Zago ya ce duk da karancin kayan aikin da suke fuskanta a ma’aikatar ba za su gajiya ba, domin gwamnatin jahar Kano ta na iya bakin kokorin ta don samar da wasu kayan aikin.
Mai unguwar Badawa Alhaji Isah Idris, ya godewa hukumar kwashe sharar, da kuma gwamnatin jahar Kano, inda ya ce daman ana yi mu su , wannan feshi lokaci zuwa lokaci , kuma suna cike da farin ciki.
Mai unguwar Badawan, a madadin sauran al’ummar yankin ya yaba wa gwamnatin Kanon, bisa namijin kokarin da ta ke yi wajen kula da lafiyar al’ummar ta a koda yaushe.
A karshe hukumar kwashe sharar ta yi fatan al’ummar yankin za su ba wa ma’aikatansu hadin kai wajen gudanar da aikin feshin, tare da tsaftace kwatocinsu.