Hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, ta ce tana shirin raba wasu kayayyakin abincin da aka kama a faɗin ƙasar, yayin da ake ci gaba da fama da matsalar karancin abinci a kasar.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar, CSC Abdullahi Maiwada, za a raba kayan abincin ne bayan an tabbatar da cewa mutane za su iya amfani da su.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an ɗauki matakin ne “domin rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta da kuma inganta hanyoyin samun kayan abinci, hukumar kwastam za ta taimaka wajen raba kayan abincin da hukumar ta kama kai tsaye.
Ƴan sandan Najeriya sun tarwatsa gugun ƴan bindiga a jihar Anambra
Yawan marasa aikin yi ya ƙaru a Najeriya bayan cire tallafin man fetur
Sanarwar ta ƙara da cewa “Za a sanar da tsarin da za a yi amfani da shi a ofisoshin hukumar da ke fadin kasar, tare da jajircewa wajen tabbatar da adalci. Mun sha alwashin cewa za a gudanar da wannan aikin domin tabbatar da cewa kayayyakin sun kai ga waɗanda suka fi bukata.”