Hukumar NAFDAC ta jagoranci garkame shagunan yan Magani 700 a Kano

Spread the love

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa reshen jihar Kano NAFDAC, ta rufe fiye da shaguna guda ɗari bakwai na masu sayar da magunguna a yankin Malam Ƙato da ke jihar.

NAFDAC ta kulle shagunan ne a daren jiya Asabar ta hanyar ƙara musu mukullai tare da liƙa takardu a jikinsu da suke nuni da cewar sune suka kulle shagunan.

Da ya ke zantawa da manema labarai, shugaban hukumar mai kula da shiyyar Kano Ƙasim Ibrahim, ya ce, sun ɗauki matakin kulle shagunan ne a ƙoƙarinsu na tabbatar da cewa, masu sayar da magungunan sun bi doka ta hanyar komawa kasuwar magani ta Dan-gwauro.


“Akwai ƙarin shaguna da za a samar a kasuwar sakamakon ƙorafin wasu masu sayar da maganin da ke cewa rashin wurin zama ne ya hana su komawa, “in ji Kasim”.

Wajiyar mu , ta ruwaito cewa, shugaban na hukumar NAFDAC mai lura da shiyyar Kano Ƙasim Ibrahim, ya ƙara da cewa, za su ci gaba da kulle shagunan masu sayar da magungunan da suke zaune ba bisa ƙa’ida ba har zuwa lokacin da suka cimma dai-daito.

Dala FM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *