Hukumar NAPTIP ta ceto mutane 470 da aka yi safarar su a jahar Katsina

Spread the love

Hukumar hana safarar mutane a Najeriya NAPTIP ta ce ta ceto mutum 470 da aka yi safararsu a Katsina a shekarar 2023.

Kwamandan NAPTIP a jihar, Musa Aliyu, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Asabar a Katsina.

A cewarsa, a cikin shekarar da ta gabata, hukumar ta kama tare da hukunta wasu mutum huɗu.

Ya ce sun samu kararraki 25 na fataucin mutane da kuma shari’o’i biyu na cin zarafin mutane.

Kwamandan NAPTIP ɗin ya kuma ce “A shekarar 2023, mun ceto mutane 470 da aka yi safararsu, tare da sake haɗa su da iyalansu.

Ya bayyana cewa, NAPTIP, tare da haɗin gwiwar Cibiyar Kula da Hijira ta Duniya (ICMPD), sun shirya jerin shirye-shiryen wayar da kan al’ummomin kan iyaka.

Ya ce sun kuma gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a tare da gwamnatin Katsina, ga shugabannin addini da na gargajiya, da kuma na matasa a kananan hukumomin Mai’adua, Baure da kuma Mashi.


” a shekarar da ta gabata hukumar mu ta ceto mutane 470 da aka yi safarar su tare da mayar da su ga iyalansu” Aliyu Musa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *