Hukumar NSCDC A Jigawa Ta Ce Jami’an Ta 1800 Ne Za Su Bayar Da tsaro A Zaben Kananan Hukumomi.

Spread the love

Hukumar  tsaron Civil Defence reshen jihar Jigawa, ta bayyana cewa ta shirya tsaf don tabbatar da tsaro, a lokacin gudanar da zaben kananan hukumomin  da za a gudanar a ranar Asabar 5 ga watan Oktoba 2024.

Sanarwar da Kakakin hukumar na Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ya bayyana cewa Jami’an za su yi aiki ne a wuraren kaɗa ƙuri’ar da wurin tattara sakamako dama sauran muhimman wuraren da suka kamata, ta yadda za a tabbatar da tsaro kafin zaben, da kuma bayan kammala wa.

Sanarwar ta kara da cewa Kwamandan hukumar a jihar Jigawa, Muhammad Danjuma, ya ce sun tanadi Jami’ai sama da 1, 800 waɗanda za su yi aiki a lokacin zaɓen.

Hukumar ta ce jami’an ta sun samu  horo na musamman, domin tinkarar duk wani ƙalubalen tsaron da ka iya tasowa a lokacin zaɓen, domin tabbatar da cewa masu kaɗa ƙuri’ar sun gudanar da zaɓen ba tare da wata fargaba ba”.

Haka kuma rundunar za ta haɗa hannu da sauran Hukumomin tsaro, wajen ganin an sami Ingantaccen tsaro a yayin zaɓen, adan haka ta gargaɗi masu ƙoƙarin kawo hargitsi da su kuka da kansu.

A ranar Asabar 5 ga watan Oktobar 2024, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Jigawa, za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *