Hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Kano ta ladaftar da wasu ma’aikatanta takwas ciki har da alkalai.
Wani kwamitin ladaftarwa na hukumar ne ya bayar da shawarar ɗaukar matakin bayan kammala bincikensa kan ƙorafe-ƙorafen da wasu suka gabatar waɗanda suka haɗa da zarge-zargen karɓar rashawa.
Kwamitin karɓar korafe-korafen jama’a na hukumar kula da harkokin shari’ar ya ɗauki matakin ladaftawar ne kan ma’aikatan shari’a su takwas ciki har da alkalan kotunan majisteret.
Kakakkin hukumar Baba Jibo Ibrahim ya ce bincike ya gano yadda wani alkalin kotun majistare ya gudanar da wata shari’a ba tare da an rubuta ta ba, abin da ya saba dokokin shari’a.
Bayanai na cewa an jima ana kokawa da jami’an kotu a jihar ga me da yadda suke karbar toshiyar baki da sauran laifuka.