Hukumar tsaron Civil Defence ta cafke matasa 2 bisa zargin fasa shago da satar buhunan Zobo 10 a Jigawa

Spread the love

Hukumar tsaron civil Defence reshen Jihar Jigawa, ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da satar buhunan zobo guda 10 a jihar.

Kakakin rundunar, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a Karamar Hukumar Hadeja.

Ya ce, an kama su ne a ranar Lahadi 21 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 8:30 na safe a unguwar Gawuna da ke Hadeja.

A cewarsa an cafke su dauke da buhu 10 na zobo wanda ake zargin na sata ne.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

Yansanda sun kama mutum takwas da suke zargi da sace É—aliban Ekiti

Mahmud, ya ce bincikensu ya nuna cewa wadanda ake zargin sun hada baki tare da fasa shagon wani mai suna Alhaji Yusuf Idris da ke Gawuna a Karamar Hukumar Hadeja.

Ya ce sun yi awon gaba da buhu 10 na zobo.

Amma kakakin ya ce, an kwato buhun zobon gaba daya, wanda darajarsa ta kai Naira N362,250.

Kazalika, ya ce an kama barayin da wasu karafa da adduna da suke amfani da su wajen fasa shagunan al’umma a yankin.

A karshe ya tabbatar da cewar da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *