Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano za ta fara binciken masu ɓoye kayan abinci

Spread the love

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta gargadi ‘yan kasuwar da ake zargi da boye kayan abinci da su daina.

Hukumar ta ce bayan korafe-korafen da ta karba daga mutane daban-daban ta umarci jami’anta su fara bincike wuraren da ake zargin an makare manyan sito-sito da kayan abinci.

Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce sun gano cewar boye kayan na daga cikin abubuwan da suke kara tsadar kayan masarufi a Kano, inda ya ce duk mutumin da suka kama to zai dandana kudarsa.

Ana dai ta zarge-zarge cewa manyan ‘yan kasuwa na boye kayan masarufi har sai ya yi tsada su fito da shi su sayar, wani abu da ake ganin yana taimakawa wajen kara dagula lamarin tsadar kayan na masarufi a Najeriya.

Kisan Nafi’u: Kotu ta yi umarnin a duba kwakwalwar Hafsat Chuchu bayan ta yi gum da bakin ta.

An gano inda ake sayar da jarirai a Anambra

‘Yan kasuwa dai a Kano da ma Najeriya na musanta zarge-zargen da ake yi musu, inda ko a makon da ya gabata sai da gamayyar kungiyar ‘yan kasuwa a birnin Kano ta yi barazanar rufe kasuwanci saboda tsadar abubuwa.

Ko a makon da ya gabata sai da daruruwan al’ummar birnin Minna na jihar Naija suka yi zanga-zangar nuna damuwa kan yanayin tsananin rayuwa da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *