Rahotanni Sun bayyana Cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da rashawa ta Jihar Kano ta gayyaci Wasu Daga Cikin jami’an Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano REMASAB
Wata majiya tace ana Zargin Cewa anyi Tafka Tafka a Hukumar ta REMASAB Musamman Wajen kudaden Shiga da da Hukumar Take Samu
Shugaban Hukumar ta REMASAB dai ambassador Alhaji Ahmad Haruna danzago Yana Samun Hutu Sakamakon Rashin Lafiya da Yayi Fama da Ita Wadda Hakan yasa Sauran Manyan Jami’an Hukumar Ke Cigaba da Tafiyar da ayyuka
Sai dai kungiyar nan Mai Suna, Kungiyar ABBA BA BUTULU BANE Ta Jihar Kano karkashin Shugaban ta Hon.Abdullahi Inuwa girma Gwale, ne Suka yaba da Matakin Hukumar ta Yaki da Cin Hanci da rashawa bisa Wannan kokari na Bincike a Hukumar REMASAB
Sun Kuma Bukaci Hukumar ta Kara zurfafa bincike Domin anyi Tafka Tafka a Wannan Hukuma ta REMASAB acewar kungiyar ta ABBA BA BUTULU BANE my