Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta gabatar da sabon kocin Super Eagles

Spread the love

An gabatar da Eric Sekou Chelle a matsayin sabon kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (Super Eagles).

Wannan na zuwa ne kimanin mako ɗaya bayan hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar ta sanar da zaɓen Chelle a matsayin sabon kocin babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya, daga cikin mutane da dama da suka nemi muƙamin.

A yanzu Eric Chelle, ɗan asalin ƙasar Mali, ya zama mai horas da ƙungiyar na 37 a tarihinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *