Hukumomin hana fasa kwabri a China sun kama wani mutum da ke ƙoƙarin fataucin macizai sama da 100 a cikin wandonsa.
An kama shi ne a lokacin da yake ƙoƙarin tsallakawa zuwa Hong Kong.
A lokacin da suke binciken aljihunsa ne suka fahimci cewa akwai micizai 104 cikin jikunan leda a rufe.
Galibinsu ƙanana ne, kuma wani bidiyon da jami’an kwastom na China suka fitar ya nuna yawan macizan.
A bara ma an taɓa kama wata mata tana ƙoƙarin fataucin macizai a rigar mama.
China dai na ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fi fataucin dabbobi.