Hukumomi a Afirka ta Kudu na shirin sauyawa fiye da mutum 150 da suka tsira daga gobarar da ta lakume wani gini da aka yi ba bisa ka’ida ba a Johannesburg.
Gobarar da ta tashi ranar Lahadi, ta halaka mutum biyu tare da raunata karin hudu.
Gobarar ta kuma daidaita iyalai da dama da ke zaune a ginin cikin muhalli mara tsafta.
An kama wata mata saboda zargin tana da hannu a iza gobarar.
Tashin gobara a gine-ginen da ake yi ba bisa ka’ida ba abu ne da ya zama ruwan dare a Johannesburg.
Ire-iren gine-ginen galibi kan fada hannun miyagu da suke ba da haya ba tare da muhalli mai kyau ba.