Hukumomi A Kano Sun Kori Jami’an Lafiya 3 Tare da Dakatar Da Wasu Sakamakon Saba Ka’idar Aiki.

Spread the love

Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta amince da korar wasu ma’aikata tare da dakatar da wasu ma’aikatan na babban asibitin Karamar Hukumar Kabo nan ta ke, bayan samun su da laifin Cazar kudade daga Marassa Lafiya da suka Wuce Kima da sauran laifuka.

Shugaban hukumar Dakta Mansur Mudi Nagoda,ne ya bayyana hakan jim kadan bayan sanya hannu kan amincewar da hukumar ta gabatar bayan kammala ziyarar da suka yi.

GLOBAL TRACKER ta ruwaito cewa Asibitin wanda babban sakataren hukumar da babban darakta na cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta jihar Kano (KNCDC) Dr. Muhammad Abbas, da darakta janar na CSACA Dr. Usman Bashir suka ziyarce su gaba daya sun nuna bacin ransu ga abinda ya faru tare da amincewar daukar matakin.

Dakta Nagoda ya yi bayanin cewa an kama jami’ai 3 na sashen X-ray suna cajin marasa lafiya 12,000 na gwajin X-ray maimakon farashin asibiti da aka amince da shi na 2,000 kuma babu wata takarda da za ta nuna a matsayin shaidar biyan kuɗin da ke barin wurin don aiwatar da gwajin lamarin da yasa ake X-ray 10 kacal a kowanne mako duk da cewa Injinan Asibitin na X-ray 2 suna aiki, daga nan sai ya amince da korar jami’an 3 nan ta ke.

Har ila yau, shugaban Hukumar ya amince da dakatar da akawun Asibitin da mai binciken kudi, da shugaban dakin gwaje-gwaje saboda sayar da kayan gwajin cuta mai karya Garkuwar jikin Dan Adam, wanda kyauta gwamnatin jihar ta ba wa cibiyoyi kuma an umarce su da su kai kansu ga hedikwatar hukumar don ci gaba da ladabtar da su.

Bugu da kari, Dakta Nagoda ya bayyana cewa dakin karbar Haihuwa na Asibitin ba shi da tsari domin ba shimfidar gado a kan gadaje, babu wani jami’in kula da gurin, haka kuma an wulakantar da wasu kayayyakin kula da lafiyar Alumma wanda wani dan majalisa ya bayar da gudummawar shekaru 4 da suka gabata, tare da nuna halin ko in kula da kayayyakin yaki da cutar COVID-19.

Shugaban ya kuma ce abin bakin ciki ne bayan mai girma gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ya dawo da kowane ma’aikacin lafiya a kan ma’aunin albashin CONHESS, amma duk da haka suna cin zalin Marassa Lafiya tare.

Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Suleiman ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce shugaban ya yi kira ga maaikatan hukumar da su rika gudanar da ayyukansu don ci gaba da kula da lafiyar Alummar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *