Hukumomi Sun Cafke Mutane 17 Da Ake Zargi Da Harkarlar Kudaden Waje A Kano.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta Kama wasu mutane 17, da ake zargi da aikata laifin siyar da kudaden waje ba bisa ka’ida ba.

Mai magana da yawun rundunar Yan Sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya aikewa da jaridar idongari. ng.

Sanarwar ta ce an kai sumamen ne a ranar Talata, tare hadin gwiwar jami’an hukumar tsaron farin kaya DSS, a Kasuwar yan Chanji ta Wappa dake yankin Karamar hukumar Fagge Kano.

Haka zalika hukumomin biyu sun gano kudaden kasashen waje, da ake hada-hadar su ta haramtacciyar hanya , da suka hada da CFA, dubu sittin da takwas sai kuma kudin Rupees Talatin na kasar India.

SP Abdullahi Kiyawa ya Kara da cewa cikin mutane 29 da suka cafke , an sallami 12 daga cikinsu saboda babu Wata shaida, da ta nuna cewa sun aikata laifin, ya yin da sauran 17 suke cin karensu babu babbaka karkashin Wata kungiya da ba a yi wa rijista ba.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya shawarci al’umma da kuma ma su hada-hadar Kasuwancin kudaden wajen, su bi Doka da oda wajen bin hanyoyin da suka dace.

Idan ba a manta ba jaridar idongari. ng, ta ruwaito mu ku cewa a watan Fabarairun 2024, rundunar yan sandan tare hadin gwiwar jami’an hukumar EFCC, sun kai sumame a wurare daban-daban na birnin Kano, inda suka kamo mutane 9 da suke harkarlar siyar da kudaden waje ba bisa ka’ida ba, wadanda tuni aka Gurfanar da su a gaban kotu.

Rundunar Yan Sandan ta ce da zarar ta kammala gudanar da bincike akan mutane 17 , da ake zargi za ta Gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *