Hukumomin Libya sun ƙi yarda jami’ai su kai wa ‘yanwasan Najeriya ziyara’

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu hukumomin Libya sun ƙi amince tawagar ofishin jakadancin ƙasar ya ziyarci ‘yanwasan Najeriya da suka maƙale a filin jirgin sama na Libyar.

MInistan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ya ce yana bin halin da tawagar ke ciki “sau da ƙafa” bayan hukumomi sun sauya akalar jirgin tawagar ta Super Eagles zuwa wani ƙaramin filin jirgi maimakon na Benghazi da aka tsara tun dafarko.

“Tun daga daren da ya wuce, ofishin jakadancin ya yi ta magana da tawagar da kuma hukumomin Libya ƙarƙashin jagorancin Jakada Stephen Anthony Awuru,” in ji ministan cikin wani saƙo a shafinsa na X.

“Duk da ƙoƙarinmu, hukumomin Libya sun ƙi ba da izinin zuwa birnin Bayda inda filin jirgin yake.”

Hukumar ƙwallon ƙafar Najeriya ta NFF ta ce ‘yanwasan nata sun shafe kusan awa 15 suna jira a filin jirgin, kafin daga baya su kwana a can.

Karanta cikakken labarin abin da ke faruwa a nan:  Ba za mu buga wasa da Libya ba – Super Eagles – Idongari.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *