Hukumomin tsaro a jahar Kano sun lashi takobin ladabtar da tunzurarrun mutanen da ke yunkurin haifar da rudani a ranar da kotun koli za ta yanke hukunci

Spread the love

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel , tare da sauran hukumomin tsaro, ya bayyana cewa sun yi duk abinda ya dace, don tabbatar da ingantaccen tsaro, gabanin yanke hukuncin kotun koli a ranar juma’a kan zaben gwamnan jahar Kano,

Kwamishinan yan sandan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudana a shelkwatar rundunar , a birnin Kano.

CP Gumel ya ce, sun tattauna da Malamai musamman limaman masallatan juma’a don su yi hudubar su ta gobe juma’a , kan muhimmancin zaman lafiya tare da kira kan kaucewa tayar da hankali da zai haifar da koma baya ga tattalin arzikin jahar Kano da kuma kimar ta, a sassan Nijeriya da ma duniya baki daya.

Ya kara da cewa, shugabannin jam’iyun siyasa , sun tabbatar mu su , da alkawarin da suka yi alkawari a kwanakin baya tare da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

” Babu wata jam’iya da ta ke goyon bayan wani ya zo ya yi barna ko su ci zarafin wani , a lokacin da wannan sakamakon zaben ya fito ko kuma aka bayyana” CP Gumel”.

Kwamishinan yan sandan CP Muhammed Usaini Gumel , ya ce tunda sun yadda da wannan, aikin su mai sauki ne, domin duk wanda ya fito babu ruwan su da cewar dan wata jam’iya ne , ko wane idan suka kama shi , za su yi amfani da damar da kundin tsarin mulkin Nijeriya da dokokin kasa ya ba su don ladabtar da shi , ba da sunan jam’iya ba.

Sai dai ya yi jan hankali ga iyaye da yan uwansu da su gargadi yayan su kar su bari wani ya yi amfani da su wajen yin abunda ba daidai ba, inda ya tabbatar da cewar duk wanda ya shigo hannunsu ba zai ji da dadi ba.

Ya kuma yi kira ga yan siyasa da suji tsoron Allah, bayan sun yi alkawarin cewar , a siyasan ce babu ruwansu , kar a samu wasu a cikin su a boye su ci amanar yayan jahar Kano , dan su dauki makamai , ko Ashana da Fetur domin yin kone-kone na cewa ba su yadda ba.

” duk wanda ya yadda aka kama shi mu ba ruwan mu da cewar wata jam’iya ce ta ba shi , umarni ya yi bisa kashin kansa kuma za mu cafke shi.

A karshe ya ce idan kuma wani dan wata jam’iya ya fito, ya ce wanda aka kama yaron su ne , to ya saba da alkawarin da aka sanya hannu , don haka za su hada dashi domin duka laifinsu daya ne kowa ye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *